Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasa, da inganta tsaro, da sake bude iyakokin kasar nana idan aka zabe shi a zabe mai zuwa.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a yayin gangamin yakin neman zabe da jam’iyyar PDP ta gudanar a filin wasa na Sani Abacha Kano.
Ya ce idan aka ba wa al’ummar kasa suka fito a ranar 25 ga wannan wata suka zabe shi har ya zama shugaban kasa zai tabbatar da cewa an bunkasa noma da yakar talauci da kuma wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa idan aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasar Nigeria zai dawo da martabar kasuwanci da aka lalata, tare da habaka walwala da tattalin arziki al’umma ta kowacce fuska.

A nasa jawabin, Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce Atiku Abubakar shi ne dan takarar da yafi chanchanta al’umma su zaba, Saboda gogewar da yake da ita a fannoni daban-daban, da kudirorin da yake da su wadanda zasu inganta Kasa.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kada kuri’unsu ga jam’iyyar PDP daga sama har kasa, wanda hakan zai baiwa jam’iyyar damar kawo cigaba don inganta rayuwar al’umma.
A jawabansu na daban, Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku/Okowa da kuma gwamnatin Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Hajiya Barka Sani sun ce PDP za ta yi nasara a zabe mai zuwa saboda mawuyacin halin da jam’iyyar APC ta jefa al’ummar Nigeria a ciki.
Gabanin zuwa filin taron sai da Alhaji Atiku Abubakar ya bude wata makarantar al’qur’ani mai girma wadda aka sanyawa suna Gwani Muhammadu Qur’anic College a garin gunduwawa dake karamar hukumar Gezawa, makarantar dai Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ne ya gina makarantar.
Yayin bude makarantar Dan takarar shugaban kasar ya yabawa Malam Shekarau bisa samar da makarantar, wadda yace zata taimaka wajen bunkasa harkokin Addinin Musulunci da tarbiyyar al’ummar jihar kano.
Dubban magoya bayan jam’iyyar PDP ne suka yi dafifi a filin wasa na Sani Abacha domin shaida taron.