Daga Auwalu Alhassan Kademi
Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ya sami jimillar kudi naira miliyan dari biyar da goma sha daya da naira dubu dari biyu da hamsin da bakwai domin gudanar da yakin neman zabe da sauran harkokin zabe da za’a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris 2023
An bayyana wadannan alkaluman ne a cikin wata sanarwa da babban mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben NNPP a kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, bayan taron liyafar cin abinci da jam’iyyar ta gudanar a daren Lahadi a Afficent Event Centre da ke Kano.

A cewar sanarwar, shugaban kwamitin tara kudaden na NNPPn Kano Hon. Dr. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ya karanta wadanda suka bayar da tallafin a daren jiya, ya bayyana matukar jin dadinsa kan dimbin tallafin da aka samu, inda ya jaddada cewa, hakan wata shaida ce dake nuna cewa mutanen Kano sun gaji da APC da PDP.

Hon. Kawu Sumaila ya kara da cewa za a yi amfani da tallafin ne wajen tallafawa yakin neman zabe da kuma harkokin zabe.
Sanarwar ta ruwaito dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP Engr. Abba K Yusuf wanda aka fi sani da (Abba Gida Gida) ya bayyana cewa irin dimbin goyon bayan da yake samu shaida ce ta yadda mutanen Kano Masu kishi na bukatar sabon salon shugabanci a jiha da kasa baki daya. Abba Gida-Gida ya jaddada kudirin sa na ganin an samar da shugabanci na gari wanda kowane dan kasa kuma mazaunin jihar Kano zai cin gajiyar tsarin shugabanci na gari.
Sanarwar ta kuma bayyana kalaman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda a jawabinsa na musamman ya ce Yan Najeriya su na da zabin kan wanda zasu zabe ko na gari ko akasin hakan, Inda ya ce masu kada kuri’a suna kara wayewa a kowace rana, kuma shawarar da suka yi na zaben jam’iyyar NNPP ita ce kadai mafita gare su saboda halin da kasar ke ciki.
Haka kuma, Babban Mai kaddamarwa Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe wanda kuma dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Rimingado da Tofa a majalisar wakilai ta tarayya ya bayar da gudunmawar kudi naira miliyan hamsin. Hon. Jobe wanda ya fito daga mazabar Gwamna Ganduje kuma a halin yanzu yana takara da dan gwamnan, ya bayyana salon siyasar Sanata Kwankwaso a matsayin na biyu a cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya.
Sanarwar ta bayyana wasu daga cikin wadanda suka bada tallafin da suka hada da Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa wanda ya bada gudunmawar naira miliyan 25, Alh. Sani Muhammad Hotoro, Naira miliyan 20, Alh. Nasiru Muhammad Danfaranshi, Naira miliyan 20, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, Naira miliyan 10, Hon. Badamasi Ayuba, Naira miliyan 10 da dai sauransu.