Ku ba ni kwanaki bakwai zan warware matsalar karancin kudi- Buhari ya fadawa gwamnonin APC

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 A ranar Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su ba shi kwanaki bakwai domin ya warware matsalar karancin kudi da ta addabi al’umma sakamakon sabon tsarin babban bankin Najeriya .
 Ya yi wannan jawabi ne ga Kungiyar Gwamnonin APC lokacin da suka je Fadar Shugaban Kasa domin neman hanyoyin magance matsalar karancin kudi da suka ce hakan na barazana ga nasarorin da gwamnatin ke samu wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar.
 Shugaba Buhari ya ce sake fasalin kudin zai kara habaka tattalin arzikin kasar tare da samar da fa’ida na dogon lokaci yayin da ya nuna shakku kan yadda bankunan suka jajirce wajen cimma nasarar manufofin.
Talla
 “Wasu bankunan ba su da inganci kawai da kansu suka damu da kansu kawai”, “ko da an kara shekara guda, matsalolin da ke da alaka da son kai da hadama ba za su bari tsarin ya tafi yadda ya dace ba.”inji Buhari
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 Ya ce ya ga rahotannin irin wahalar da karancin kudaden suka sanya kananan an kasuwa da masu karamin karfi a gidajen talabijin, ya kuma ba da tabbacin nan da kwanaki 10 masu zuwa wajen magance matsaloli da wahalar da ake fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...