Daga Ibrahim Abubakar Diso
Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta kama wasu matasa guda biyu da ake zargi da garkuwa da wasu Yara guda 2 har suka nemi a tura musu Naira Miliyan 20 a matsayin kudin Fansa.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, yace rundunar ta yi nasarar kama matasan ne lokacin da suka aikowa da Iyayen yaran da suka sace da wasika mai dauke da lambar wayarsu da Kuma account number domin tura musu kuɗin fansa.
Yace Matasa Masu suna Nura Auwal Mai shekaru 22 mazaunin Rijiyar lemo da abokin sa Abubakar Lawan mai shekaru 22 mazaunin Bachirawa a kano sun bukaci a iyayen yaran da su basi Naira Miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa, yayin da daga bisa ni suka Amince zasu karbi Naira Miliyan 4 kafin su sake su.

SP Kiyawa yace tuni wadanda ake zargi sun tabbatar da cewa sun aikata laifin, kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar kano CP Mamman Dauda ya bada umarnin fadada bincike da Kuma gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci daidai da laifin su.

Kiyawa yace tuni aka ceto yaran wadanda kowannen su bai wuce shekaru 3 zuwa 4 a Wani kango Inda aka ajiye su, bayan sun karbi korafi daga wani Auwal Sale tun a ranar 26 ga watan Janairu 2023.