Karancin Man Fetur ka iya shafar zabe a Nigeria – INEC

Date:

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce matsalar ƙaramncin man fetur da ƙasar ke fuskanta ka iya shafar tsare-tsaren hukumar game da za ta shirya zaɓen ƙasar da ke tafe.

Shugaban Hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja a lokacin taron tuntuɓa tsakanin hukumar da ƙungiyoyin direbobin haya na ƙasar waɗanda suka haɗar da NARTO da NURTW da sauransu.

“Hukumar zaɓe tana tare da ku game da kokenku na ƙarancin man fetur da ƙasar nan ke fuskanta, da yadda hakan zai shafi hakar sufuri musamman a ranar zaɓe,” in ji Mahmood.

Ya ƙara da cewa “magana ta gaskiya ita ce rashin wadataccen man zai shafi shirye-shiryenmu”. Inji Farfesa Mahmoud

Talla

Shugaban hukumar ya ce dangane da wannan dalili , hukumar zaɓe za ta gana da kamfanin mai na ƙasa NNPCL domin duba hanyoyin da ya kamata a bi wajen magance wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...