Idan Atiku ya zo kano yakin neman zabe, zai bude makarantar haddar al’qur’ani mai daukar mutane 500

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar zai gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a Kano ranar 9 ga Fabrairu, 2023.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban kwamitin yada labarai Dr. Sule Ya’u Sule ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai Kano.
 Ya ce dan takarar shugaban kasa zai yi wa jama’ar Kano jawabi kan tsare-tsarensa da manufofin da zai aiwatar idan aka zabe shi.
Talla
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
 “Wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun zo kano sun tafi, wasu rawa kawai sukai, wasu Kuma kofin shayi ma ya gagaresu rikewa, amma yanzu lokaci yayi da Atiku Abubakar zai shigo Kano, don haka akwai bukatar kowa ya zo domin ganewa idanun sa, yadda Atiku zai fayyace manufofin da tsare-tsaren sa, don haka duk muna gayyatarku, ku zo ku ga bambanci,” in ji Dr. Sule Ya’u.
 Ya ce “Atiku zai yi taron ne a filin wasa na Sani Abacha Kofar Mata da ke Kano a ranar 9 ga Fabrairu, 2023 da karfe 11:00 na safe”.
 A cewar Sule Yau Sule dan takarar shugaban kasa zai kuma kaddamar da makarantar haddar Alkur’ani mai girma wadda zata ɗauki mutane akalla 500 wanda Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya gina a garin gunduwawa dake karamar hukumar Gezawa .
” Idan an bude makarantar zata rika koyar da haddar al’qur’ani mai girma ga yara matasa a cikin watanni 6 , Kuma an samar da dukkanin wani abun bukatar dalibai a makarantar Saboda makarantar kwanace”. A cewar Dr. Sule Ya’u Sule
 Ya ce za a kaddamar da aikin ne a yayin ziyarar da Atiku zai kai jihar kano a wani bangare na shirye-shiryen yakin neman zabensa gabanin zaben shugaban kasa.
Dr. Sule Ya’u Sule ya bada tabbacin zasu zasu gudanar da taron lami lafiya Saboda su kowa yasan basa tsokanar kowa Kowa, don haka mun yi dukkanin wasu tsare-tsare don ganin an yi taron kano Lafiya kamar yadda ake yi a sauran jihohin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...