Kotu ta bayar da umarnin kama Shugaban APC na Kano

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

 Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin kamawa, bincike da kuma gurfanar da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas.
 A karar da Mahmoud Lamido ya shigar, ana zargin shugaban jam’iyyar da yin kalaman tunzura al’umma, da kawo cikas ga zaman lafiya, da kuma kalaman da basu dace.
 Lawan Lamido Bashir Yusuf Muhammad, ya shaida wa kotun cewa Abdullahi Abbas ya yi barazanar kashe wanda yake karewa ta wayar tarho.
Talla
 Alkalin kotun, Mai shari’a S. A. Amobeda, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu 2023.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Jam’iyyar NNPP ta yi murna da wannan cigaba kasancewar hakan zai kara kare damakaradiyya, saboda wanda ake karar ta jima yana kalaman tunzura al’umma.
Babban Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar NNPP a kano Sanusi Bature Dawakin Tofa yace a kwanakin baya wata kotu daban ta baiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar kano umarnin kama Abdullahi Abbas saboda irin kalaman tunzura al’umma da yake yi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...