Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Jami’an Rundunar ‘yan sanda sun kama fitacciyar jarumar wasan barkwanci ta TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya a Otal din Tahir da ke Kano.
‘Yan sandan sun kama ta ne a lokacin da take kokarin kama daki ga wasu bakinta da zasu zo daga nesa domin halartar taron bikin Birthday din ta .

A watan Satumban shekarar da ta gabata ne wata kotun shari’ar Musulunci ta rubutawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano wasika da ya kama Murja Kunya tare da wasu ‘yan TikToke bisa laifin lalata tarbiyyar al’umma.

Sauran TikTokers da ke cikin wasikar sun hada da Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiana.