Jama’ar Kura Madobi da Garun Mallam Sun fid da Musa Iliyasu Kwankwaso kunya- Abdullahi Abbas

Date:

Daga Nura Abubakar Cele

 

 

A jiya Asabar ne dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da tawagar yakin neman zaben sa suka shiga kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam don neman goyon bayan al’ummar yankin.

 

Babu shakka daga yadda al’ummar yankin suka fito a dukkanin kananan hukumomin uku ya nuna yadda jama’ar suka karbi jam’iyyar APC, saboda farin jinin da dan takarar majalisar tarayya na kananan hukumomin Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso yake da shi a wajen al’umma.

Talla
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Yawan al’ummar da suka fito ne a dukkanin kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam ya kayatar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas, hakan tasa ya yabawa Musa Iliyasu saboda irin kaunar da yaga an nunawa yan takarar jam’iyyar APC a dukkanin matakai .

 

” Babu Shakka yawan mutanen da suka fito domin tarbar mu da nuna mana kauna a dukkanin kananan hukumomin da muka shiga a yau (Asabar), ya karamin kwarin gwiwar musa Iliyasu Kwankwaso zai lashe zaben sa cikin sauki, sannan suma sauran yan takarar jam’iyyar mu na APC duk zasu cinye zaben su a lokacin zaben dake tafe”. Inji Abdullahi Abbas

 

Abdullahi Abbas yace dama dan takarar gwamnan kano na jam’iyyar NNPP ya karaya da karamar hukumar gwale, hakan tasa ya fara tunanin ko zai iya lashe zabe a yankin Mai gidansa , amma wannan taro yasa na fahimci cewa mai gidan nasa ma Musa Iliyasu Kwankwaso ya hana shi sakat a yankin, don haka muna yaba maka Musa Iliyasu”.

 

A jawabinsa dan takarar dan majalisar tarayya na kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC Hon Musa Iliyasu Kwankwaso ya yabawa al’ummar yankin saboda kaunar da suka nuna masa, Inda yace hakan alamu ne na nasara ga jam’iyyar APC a yankin da kano baki daya.

 

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci al’ummar yankin da a ranar zabe su fito da wuri domin zabar jam’iyyar APC tun daga sama har kasa.

 

Dan takarar gwamnan kano a APC da mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Hon. Murtala Sule Garo ne suka jagoranci mika tuta ga Hon . Musa Iliyasu Kwankwaso da sauran yan takarar majalisar jihar a yankin.

Yadda Musa Iliyasu Kwankwaso ya karbi tuta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...