Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Duk da dakatar da ziyararsa da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi, akwai yiwuwar Shugaban Ƙasa, Muhammadu ya, zai ziyarci jihar gobe Litinin kamar yadda aka tsara.
Wani bincike ya nuna cewa Shugaba Buhari bai gamsu da dalilin da gwamnatin jihar Kano ta bayar na dakatar da ziyara tasa ba.
A wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jiha, Gwamna Ganduje ya shawarci Shugaba Buhari da ya dakatar da ziyarar, duba da wasu dalilai .

A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya aikowa kadaura24 yace matakin da gwamnatin kano ta dauka ya sami goyon bayan dukkanin masu ruwa da tsaki a kano.

Jaridar Sunday Tribune ta gano cewa Shugaba Buhari ya dage cewa shi fa ba abin da zai hana shi kawo wannan ziyara.
A gobe Litinin ne dai ake sa ran Buhari zai shigo Kano domin bude tashar tsandauri ta Dala, wadda gwamnatin tarayya ta samar karkashin jagorancin sa kamar yadda ake ta sanarwa a kafafen yada labarai.
Banda ayyukan da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, akwai wasu ayyuka da gwamnatin tarayya ta gudanar waɗanda aka tsara Shugaba Buhari zai ƙaddamar.
Shugaban ya yanke shawarar cewa zai zo Kano don ƙaddamar da ayyukan na gwamnatin tarayya.
Tuni tawagar Shugaban Ƙasar ta dira a Kano, kuma har zuwa ranar Asabar da daddare ba a ce su bar Kano zuwa Abuja ba.