Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana wahalar man fetur da ake fuskanta da kuma batun sauyin kudade da cewa makarkashiya ce ake yiwa jam’iyyar APC don kar taci zaben mai zuwa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abeokuta, jihar Ogun, yayin yakin neman zabensa.

Yace bai adace a irin wannan lokaci a fito da manufofin da zasu wahalar da al’umma ba kuma har ma su hana su fito domin kada kuri’a a zaben watan gobe dake tafe.
Ya ce zabukan da ke tafe za su kasance mafi girman juyin juya hali.
“Ba sa son a gudanar da wannan zabe.
Suna son yi mana zagon kasa a zaben.
Shin za ku kyale su”,
Tinubu ya tambayi magoya bayan da suka hallara a wurin taron, inda suka amsa da “A’a.”
Tinubu ya sha alwashin cewa “za mu yi amfani da PVC mu karbe gwamnati daga hannunsu,” kamar yadda ya nuna cewa zabe mai zuwa zai zama “juyin juya hali.”
“Ko da sun ce babu mai, za mu yi tattaki don kada kuri’a.