Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta karancin sabbin kudaden Naira kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke zargin.
Gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele, wanda Musa Jimoh, Daraktan sashen kula da tsarin biyan kudi na bankin ya wakilta, ya musanta zargin a wani taron manema labarai a Jos.

“CBN ta mika wa bankunan kasuwanci sabbin takardun kudi domin rabawa a bankunan da kuma injinan ATM .
“Wannan shi ne tsarin da muka yi don ba da damar yada kudaden cikin saurin kuma muna son ba da shawarar bankunan kasuwanci da su daina ware kudaden daga jama’a ko kuma su fuskanci tsauraran takunkumi,” in ji shi.
