Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wani abun al’ajabi ya faru a kan titin zuwa Kano dake jihar Kaduna, Inda aka baiwa yan wasu al’amajirai sadaka da cikin tsofaffin kudin da aka sabunta suka ki karba saboda ba sabo bane.
” Ina sauka daga mota sai naga mutanen uku sun zo suna yi min bara sai na bude jakar kudina (Wallet) na dauko naira 1000 na basu, kawai sai naga sun Kalli juna ba ce min komai ba sai suka juya suka bani wurin ,abun ya bani mamaki matuka”. A cewar Caleb
Wakilin Majiyar Kadaura24 ya rawaito cewa lamarin ya faru ne akan idon sa, Inda wani matashi ya baiwa almajiran sadakar naira 1000 suka ki karba saboda tsohuwa ce .
wanda ya bada sadakat matashine mai suna Caleb yace abun ya bashi mamaki kasancewar sadakar kudin ya basu Amma suka ki karba don sun ga tsofaffine , “ga shi kuma ni bani da Sabbin kudin da aka sauyawa fasali”.

