Daga Halima Musa Sabaru
Sanatan kano ta Kudu Kabiru Ibrahim Gaya ya ƙalubalanci rashin Kara wa’adi da tsoffin kuɗade a Nigeria, sakamakon mawuyacin halin da al’umma suka shiga.
“Wannan tsarin bama goyon bayan sa saboda babu sauki a cikin sa, babban abun jin tausayin ma shi ne mutanen mu na karkara saboda su ne suke da karamin karfi kuma basu da masaniyar yadda zasu Kai kudaden su banki”. Inji Sanata Gaya
Kadaura24 ta rawaito Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai.

Yace a matsayin su na ‘yan majalisa sun yi iya bakin kokarin su don ganin an kara wa’adin karbar tsofaffin kuɗin domin a saukaka talakawa Masu karamin karfi.

- “Ana cewa wai saboda yan siyasa aka dau wanann mataki, Amma ya kamata a sani yan siyasa masu takara tun watanni uku da suka gabata suka tanadi abun da suke bukata, akwai talakawa ne zasu sha wahala”. Inji Gaya
Sanata Kabiru Gaya ya kara da cewa yana kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta umartar gwamnan babban bankin kasa daya Kara wa’adin karbar tsofaffin kuɗin ko dan a saukakawa kananan yan kasuwa da talakawa.
” Kamata yayi abi a hankali wajen janye tsaffin kuɗin har sai sabbin kudaden da aka saura fasalinsu wadata, amma wannan tsarin gaskiya akwai matsala sosai , kuma wani zalunci da ake shi ne Kaba da Naira dubu 20 tsofaffi a baka Naira dubu 10 Sabbin wannan zalunci ne”. A cewar Sanata Gaya