Majalisar Dokokin Najeriya a ranar Talata ta gayyaci shuagabannin bankunan kasuwanci domin bayyana a gabanta a ranar Laraba kan karancin sabbin takardun kuɗi da ake fuskanta.
Babban Darekta kuma Shugaban Bankunan karkashin kwamitin bankuna, za su haɗu da kwamitin wucin gadi na Majalisar da shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado-Doguwa ke jagoranta.

A wani zama da majalisar ta yi a yau Talata, ta yanke shawarar gayyato bankunan domin su zo gabanta su yi bayani kan matsalolin ƙarancin kuɗi da ake samu daga Babban Bankin Najeriya, inda daga baya za ta gayyato shugabannin na CBN domin zuwa amsa tambayoyi.
Majalisar ta kuma bukaci a tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da wata shida.
