Daga Ali Abdullahi Fagge
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin dorawa da kuma inganta tsaro da zaman lafiya da ake samu a jihar idan aka zabe shi a matsayin Gwamna a zabe mai zuwa.
Gawuna ya bayyana hakan ne yayin wani taro da yan takarar gwamnan kano, wanda jami’ar Bayero da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya a dakin taro na Sa’adu Zungur, gidan Mambayya a kano.
Ya ce Tsaro yana kawo ci gaba da walwala ga al’umma, don haka zai kara hadin kai da jami’an tsaro domin ganin al’ummar Kano sun ci gaba da zama tare cikin kwanciyar hankali da lumana.

Gawuna ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kuma ci gaba da bunkasa a fannin ilimi ta hanyar samar da kayan koyo da koyarwa, horar da malamai da kuma karfafa manhajar karatu tare da sana’o’i, kasuwanci da kuma hada kan al’umma.

Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24,yace Gawuna ya kuma yi bayanin yadda zai inganta fanni hakar ma’adanai wanda hakan zai bada gudunmawa sosai wajen samawa matasa aiyukan yi da samun kudaden haraji.
Mataimakin gwamnan ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa matasa da mata ta hanyar basu horon sana’o’i da jarin da zai taimake su wajen inganta Rayuwar
Sai dai ya ba da tabbacin ba da kulawa ga fannin Lafiya, Ruwa, Noma da Muhalli.