Amb.Dr.Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya bukaci al’ummar musamman mawadata da su rika tallafawa Marayun dake gidan marayu na Nasarawa a jihar kano domin neman yardar Allah subhanallahu wata’ala.
Falakin Shinkafin ya bayyana hakan ne yayin da ya gudanar da murna bikin zagayowar ranar haihuwar sa, wanda ya gudana tare da marayun dake gidan marayu n Nasarawa.
Talla
Yace ya zabi gudanar da bikin ranar haihuwar tashi ne na wannan shekarar tare da marayun ne saboda tausaya musu sakamakon halin da suka tsinci kawunansu a ciki.
” Wandan nan marayun ni a wajena sun fi ya’yan da na haifa saboda Basu suka zabawa kansu shiga halin da suke ciki ba, kuma nayi imani duk wanda ya jibanci al’amuran ‘ya’yan wasu to shi Kuma sai Allah ya jibanci na ‘ya’yan sa koda bayan baya raye”. Inji jarman matasan arewa
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Falakin Shinkafin yace akwai butakar al’umma su rika ziyartar marayun don tallafa musu domin neman yardar Allah duniya da lahita.
” Babu shakka na gamsu da yadda gwamnatin jihar kano take baiwa yaran nan kulawa, Amma duk da haka akwai bukatar sauran al’umma su rika tallafawa Marayun, Kuma nima nayi alkawarin lokacin zuwa lokacin zan rika ziyartar wannan gidan domin bada gudummawata dai-dai gwargwadon ikona”. Falakin Shinkafi
Da take nata jawabin kwamishiniyar harkokin mata ta jihar kano Dr. Zahra’u Muhd Umar ta yabawa Falakin Shinkafin bisa wannan abun alkhairi da ya kaiwa marayun, Inda tace akwai bukatar sauran Matasa su yi koyi da shi.
Malama Zahra’u Muhd ta kawo hadisan ma’aiki (S A W) wadanda suke bayyana falalar tallafawa irin wadancan yara, ta Kuma yi masa addu’o’in samin nasara a Rayuwar sa.
Falakin Shinkafi tare da wasu marayu
” A mafi yawan lokaci idan ranar haihuwar wasu matasan ta zo sukan yi murnar ne ta hanyar shagalta dayin biki da kade-kade da Raye-raye, tare da yanka cake ba tare da tunawa da bayin Allah da su kulawa ma kawai suke fuskanta”. Malama Zahra’u Muhd
Falakin Shinkafi Amb.Dr.Yunusa Hamza yayin da ya ziyarci gidan marayun dake Nasarawa, ya kai musu kayan amfani na yau da kullum wadanda suka hadar da sabulu wanka dana wanki , panpars ,tissue,alawa,hoda ,lemo , da kayan wasan yara, kudi da dai sauransu.