Kotu ta aike da wasu alkalai gidan yari bisa zargin cin kuɗin marayu a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Wata Kotun Majistare mai lamba 14 a Jihar Kano ta aike da wasu alkalai da ma’aikatan Hukumar Shari’a gidan yari, bisa zarginsu da wawure Naira miliyan 99.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun, karkashin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ta aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wadanda mallakin wasu marayu ne.

 

Tun da fari dai Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wasu alkalai da kuma ma’aikatan Hukumar Shari’ar Musulunci a gaban kotun.

 

Talla

Wadanda aka gurfanar a gaban kotun sun hada da Sani Ali da Sani Uba Ali da Bashir Baffa da Gazzali Wada da Hadi Tijjani Mu’azu da Alkasim Abdullahi da Yusuf Abdullahi da kuma Mustafah Bala.

 

Sauran sun hada da Jaafar Ahmad da Adamu Balarabe da Aminu Abdulhadi da Abdullahi Sulaiman Zango da Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa da kuma Usaina Imam.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Takardar karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira miliyan 99, laifukan da dukkaninsu suka musanta.

 

Mai gabar da kara, Barista Zaharaddin Kofar Mata, ya roki kotun da ta ba su wata ranar domin sake gabatar da su a gaban kotun tare da kawo shaida.

 

Sai dai lauyoyin wadanda ake kara bakinsu ya zo daya a kan neman beli, kodayake kotun ta ki ta bayar da belin nasu, inda ta ce za ta bayyana matsayinta game da rokon belin a zamanta na gaba.

 

Daga nan ne sai alkalin ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar daya ga watan Fabrairu, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...