Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kimanin mutane 25 ne suka rasu sakamakon kamuwa da wata sabuwar cuta mai diphtheria wadda take shafar hanci da makogaro .
SOLACEBASE ta rawaito cewa cutar wadda take kashe kananan yara da aka fara gano ta a Kano a karshen shekarar da ta gabata, kuma ana kula da wadanda suka kamu da cutar a Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, AKTH, a Kano.
Kwararrun likitocin sun ce cutar diphtheria cuta ce mai tsanani da ta ke shafar hanci da makogwaro da ake iya yin rigakafinta cikin sauki .

Jaridar ta gano cewa an fara samun cutar ne daga karamar hukumar Ungogo da ke Kano.
a wata ganawa da jaridar kadaura24 ta yi da Mai unguwar Bare-Bari dake karamar hukumar Ungoggo yace a yankin sa kadai cutar ta hallaka mutene 11 .

A cewar bayanan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da jaridar ta wallafa, game da bullar cutar, an samu rahoton mutane 58 da ake zargin sun kamu da cutar, 6 kuma an kwantar da su sannan kuma marasa lafiya 25 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar diphtheria a ranar 13 ga Janairu, 2023.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa wannan jarida cewa, da samun labarin bullar cutar, nan da nan Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Kasa, NCDC, ta tura jami’ai zuwa Kano, domin samar da wani kwamiti da za su gudanar da bincike akan bullar cutar amai da gudawa, da bayar da tallafin fasaha da kuma sake farfado da aikin cibiyar aiki don magance matsalar.
Wani mai ba da shawara kan harkokin kiwon lafiya da ya nemi a sakaya sunansa ya danganta bullar cutar da gaza yiwa mutane allurar rigakafin da aka saba yi a Kano.
Masanin ya ce, akwai karancin aikin rigakafi a Kano, wanda shi ne babbar hanyar rigakafin barkewar cutar, tare da karancin wayar da kan jama’a aka cutar .
Ka ga da a ce an gudanar da rigakafi sannan an fadakar da mazauna yankin, da hakan zai rage yaduwar cutar a tsakanin yara,’’ in ji likitan
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga SOLACEBASE a ranar Alhamis, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce kwamitin gaggawa na jihar yayi taro akan lamarin a safiyar yau Alhamis domin tantance alkaluman wadanda suka mutu, da kuma duba matakan shawo kan lamarin.
“Bai kamata mutane su firgita ba amma idan sun ga wani zazzabi da ba a saba gani ba, ya kamata su ziyarci asibiti mafi kusa da su.” a cewar kwamishinan
”Mun riga mun fara wayar da kan jama’a game da cutar.”