Daga Rahama Umar Kwaru
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana dangantakar dake tsakanin jihar Kano da jihar Borno da cewa alakace Mai dunbun tarihi tun kokacin kafa Masarautar Daular Borno.
Sarkin ya bayyana haka ne ta bakin madakin Kano Alhaji Yusuf Labahani Chidari yayin da ya karbi bakuncin tawagar wakilin Shehun Borno a jihar Kano Mai Mustapha Lawan yayin da suka ziyarci masarautar.

Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24,ya ce Alhaji Yusuf Ibrahim Labahani Cigari yace Alakar mai dadadden tarihin da ta shafi harkar auratayya da kasuwanci da kuma addini, ya godewa al’ummar jihar Borno mazauna jihar Kano bisa Zama cikin kwanciyar hankali da suke da alummar jihar Kano.

Anasa jawabin wakilin Shehun Borno Mai Mustapha Lawan ya ce sun ziyarci fadar Sarkin Kano ne domin taya shi murnar samun lambar girmamawa da shugaban kasa ya Bashi ta CFR da wacce aka bashi a kasar waje.
Hakiman da suka wakilci sarkin Kano yayin karbar bakin sun Hadar da Dan Goriban Kano da walin Kano da Turakin kano da sarkin Dawaki Mai tuta da kuma Malam Awaisu Abbas Sunusi.