Daga Mukhtar Dahiru Rigachikun
Yayin da aka fara shirye-shiryen noman rani na shekarar 2023 a fadin kasar nan, kungiyar Mata Manoma ta Kasa (WOFAN) ta fara rabon kayan amfanin gona ga kananan manoma 225,000 a fadin Jihohin Arewa 10 (ciki har da FCT).
Wata sanarwa da babbar Daraktar kungiyar Matan Manoma (WOFAN), Hajiya Salamatu Garba ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ta kuma aika wa SOLACE BASE, ta ce wannan wani bangare ne na shirin samar da ayyukan yi ga matasa a fannin noma.

sanarwar ta kara da cewa, matasa 225,000 na daga cikin abokan hulda 675,000 da shirin ICON2 yake so ya cimma a tsawon shekaru uku, tun daga shekara ta 2023.

“Bayan shekara ta uku, WOFAN za ta ci gaba da tallafa wa abokan huldar 675,000 na tsawon shekaru biyu don karfafa hanyoyin samun kudi da kasuwanci mai riba,” in ji sanarwar.
Ya ce kayayyakin sun hada da ingantaccen iri 300,000, da buhu 42,000 na taki mai nauyin 50kg, sai lita 36,000 ta maganin kashe kwari da kayan sarrafa iraruwa, wanda za a samar da su ga kungiyoyi wanda matasa 225,000 zasu samu domin noman rani na shekara ta 1 (wato, 2023) .
Ana sa ran tallafin zai samar da aikin yi ga akalla matasa 675,000 ta kai tsaye, ya yin da kuma wasu mutane 675,000 da wasu miliyoyin ma zasu sami ldamammakin ta hanyoyi daban-daban a cikin wadannan shekaru biyar.”
SOLACEBASE ta ruwaito cewa ICON2 Project wanda MasterCard Foundation (MCF) da WOFAN suka dauki nauyin gudanar da shi tare da tallafin wasu abokan hulda wajen aiwatar da shirin a Adamawa, Bauchi, Benue, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Nasarawa, Plateau Jihohin da kuma babban birnin tarayya FCT. .