Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar kasuwar Abinci ta Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa, ta bayyana gamsuwarta bisa tsarin da Babban Bakin Najeriya (CBN) ya bijiro da shi a kasar nan na takaita hada-hadar kudade a hannun al’umma.
Sakataren kungiyar wanda kuma shi ne garkuwar matasan Arewacin Najeriya, Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi ne,ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano .

Rabiu Abubakar Tumfafi, yace takaita zirga-zirgar kudaden a hannun al’umma zai taimakawa yan kasuwa wajen aiwatar da kasuwancinsu na yau da kullum cikin sauƙi kuma daidai da Zamani .
Garkuwar matasan ya kara da cewa, tsarin zai taimaka yan kasuwa wajen inganta harkokin kasuwancin su da kuma magance matsalolin da yan kasuwa suke bukata musamman na barayi da sauran asarori da suke yayin harkarsu ta fatauci.

” Ina amfani da wannan damar wajen jan hankalin matasan Arewacin Najeriya da su kaucewa shiga cikin bangar siyasa, musamman saboda karatowa Babban zabe, Wanda ya jaddada cewa, kamata yayi matasan su yi amfani da wannan dama, wajen zaben shugabanni nagari da za su taimakawa rayuwarsu da alummar kasa baki daya”.
- ” Daliban da suka kammala karatu basu samu ayyukan yi ba, Ina fatan zasu bijiro da managartan tsare-tsaren inganta rayuwa da farfado da tattalin Najeriya, Saboda yadda Nigeria ta samu kanta a wani yanayi da take bukatar matasa su kawo dauki domin sune shugabannin gobe”. Inji Rabi’u Tumfafi
Tumfafi ya kara da cewa, waji ne wayarwa da kan matasa da basu shawarwari da za su Nesanta Kansu da shiga cikin bangar siyasa duba da halin da al’ummar kasar nan suka samu kawunsu a ciki na matsin rayuwa ,Wanda akwai bukatar jan hankulansu dangane da al’amuran rayuwa na yau da kullum.
Yace idan matasa suna bari ana amfani da su wajen cin mutuncin wasu abokanan burmin siyasa ta hanyar basu muggun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan da za su iya haifar da tarzoma da hargitsi tsakanin al’umma Wanda zai kai ga rasa rayukan al’umma.
Daga karshe ya yabawa matasan Arewacin Najeriya, bisa yadda suka jajirce wajen neman ilimi saboda da ilimi ne ake samun ci gaba a koina a duniya.