Akwai yiwuwar mutane sama da Miliyan 25 su fuskanci yunwa a Nigeria – Bincike

Date:

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar faɗawa halin yunwa tsakanin watan Yuni da kuma Agustan 2023 muddin ba a dauki matakin gaggawa ba.

 

Rahoton wanda kungiyar Cadre Harmonisé ta fitar, wadda kungiya ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa wajen samar da abinci mai gina jiki, ya nuna cewa ƙasar na ci gaba da fama da rikice-rikice da sauyin yanayi da kuma hauhwarar farashin kayan abinci.

 

A cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumar noma da samar da abinci da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da hukumar bayar da agaji suka fitar, ta ce hakan ya nuna ƙaruwa a mutane miliyan 17 da ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yanzu.

 

Sanarwar ta kuma lura cewa an ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-baya ya shafi aikin samar da abinci a yankin arewa maso gabas a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe da kuma matsalar ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Neja.

 

Sanarwar ta ce Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta ruwaito cewa matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a shekarar 2022, ya lalata kadada 676,000 na gonaki wanda kuma ya kawo raguwa a abin da mutane suka girba da janyo ƙaruwar barazanar matsalar ƙarancin abinci ga iyalai a faɗin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...