Daga Ibrahim Sidi Jega
Shugaban Karamar Hukumar Mulki Ta Gwandu Hon Bello Atiku Kurya Ya Ziyararci Garin Malisa a Inda Hadarin Ya Akku, Kana Ya Ziyararci Babban Asibitin Garin Gwandu Domin Ya Ga Wudanda Suka Samu Raunukka da Kuma Wudanda Suka Rasa Rayukkan Su Duk Asanadiyyar Hatsarin.
Haka Kuma Yayin da Yake Zantawa da Shugaban Assibitin Garin Gwandu Doctor Aliyu, Ya Bayyana Masa Cewa Kimanin Mutum 26 Ne Suka Samu Raunukka Wudanda Ahalin Yanzu Suna Karbar Magani, Ayayin da Kuma Mutum 16 Suka Rigamu Gidan Gaskiya.

Abisa Baynin da Aka Samu Babbar Motar Ta Taso Daga Garin Illela Ta Jahar Sokoto, Ta Dauko Lodin Shanu 70 Tare Mutane 40 Zuwa Babban Birnin Legas Domin Gudanarda Kasuwancin Su, Ansamu Halartar Kwamishinan ”Yan Sandan Jahar Kebbi Tare da Babban Kwamandan Kare Hadurra Na Jahar Kebbi da shugaban karamar hukumar Gwandu Hon. Kurya duk sunje wajan domin ganin Yanda Lamarin Ya Faru.

Hon Kurya ya baya bada tallafin Kudi Ga Wudanda suka samu raunuka da kuma wasu Kudaden domin jigilar wadanda suka rasa rayukkan su zuwa ga Iyalan su.