Dan Majalisar Wudil da Garko ya Bada Tallafin Naira Dubu 650 ga Wata Islamiyya a Darki

Date:

Daga Shu’aibu Abdullahi Hayewa

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil, ya ba da gudunmawar Naira dubu dari shida da hamsin, ga wata makarantar Islamiyya mai suna Darul Arkam dake garin darki a karamar hukumar Wudil.

 

Dan majalisar ya bayyana bada tallafin ne lokacin da ya halarci taron bikin saukar dalibai 40 na makarantar da suka sauke al-qur’ani mai girma .

 

Yace ya bayar da gudunmawar ne domin a karasa aikin ginin makarantar na din-dindin, domin su sami sukunin gudanar da koyo da koyarwa a makarantar a kowanne lokaci ba tare da matsala ba.

Talla

” A baya na saya muku filin da ake wanann ginin, yanzu kuma ga gudunmawar Naira dubu dari shida da hamsin, kuma Ina baku tabbacin zan cigaba da bada gudunmawa har sai an kammala wannan gini, don a cigaba da koyar da karatun al-qur’ani a wannan wuri”. Ini Dan Majalisar

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Engr. Muhammad Ali Wudil, ya ce daga cikin dubu dari shida da hamsin da ya baiwa makarantar lakadan ba ajalan ba, dubu dari na daliban da suka yi saukar ne, dubu hamsin kuma na Malaman makarantar yayin Kuma da ya bada naira dubu dari biyar don karasa ginin makarantar.

 

Ya yabawa malaman makarantar bisa yadda suka dage wajen koyar da daliban karatun al-qur’ani mai girma tare kuma da yin kira ga sauran daliban makarantar da su Kara dagewa don ganin suma sun sauke al-Qur’anin kamar yadda yan uwansu sukai.

 

Dan majalisar ya kuma Sha alwashin cigaba da tallafawa al’ummar yankin musamman ta fuskar karatun al-qur’ani da sauran Ilimin addini musulunci, wanda sai da shi ne dan Adam yake iya bautawa Allah subhanallahu wata’ala.q

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...