Hukumomi a Afirka ta Kudu na neman wata Damisa ruwa a jallo, da ta tsere daga hannun ubangidanta a yankin Walkerville da ke kudancin birnin Johannesburg.
Damisar ta tsere ne lokacin da katangar gidan ta fadi a daren Asabar, kamar yadda kafar yada labaran yankin ta bayyana.

Wasu rahotannin sun ce Damisar ta kai wa wani mutum hari, ta kuma yi ajalin wani kare da jikkata guda.

Hukumomin da ke kula da dabbobi a Afirka ta Kudu, sun gargadi mutane kar su kuskura su tunkari damisar idan sun gamu saboda dalilai na tsaro da hadarin da ke cikin hakan.