Daga Halima Musa Sabaru
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta SSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya CBN inda suka mamaye ofishin gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an yi artabu tsakanin jami’an SSS da Mista Emefiele kan zargin bada kudaden ta’addanci.

A baya dai hukumar ta nemi kotu ta kama Mista Emefiele amma ya fita kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.

Sai dai a watan Disamba ne wata babba a kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS kamawa ko gayyata, ko kuma tsare Mista Emefiele.
Jami’an SSS da suka isa hedikwatar CBN a ranar Litinin din nan, sun shiga da motoci kusan 20 dauke da makamai.
Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Mista Emefiele.
Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har yanzu bai amsa tambayar da yan jarida suka aika masa .