Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kamfanin siminti na Dangote ya yaye mata a kalla 40 harkokin dinke-dinke a jihar Kogi.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye wadanda aka koyawa sana’o’in a ranar Alhamis a Obajana, wani Darakta a Kamfanin Dangote Cement Plc, Obajana, Mista JV Gungune, ya ce shirin koyar da sana’o’in anyi shi ne da nufin tallafa wa gwamnati a kokarinta na samar da ayyukan yi ga matasa .
Mista Gungune ya ce duk da cewa tsarin samar da ayyukan yi ya daidai da hangen nesa da manufofin kamfanin, Amma ba zai iya yin shi kadai ba, kuma ba zai iya daukar kowa aiki ba, ya kara da cewa shirin samar da ayyukan yi wata hanya ce ta samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar Kogi.

Daraktan ya ce wadanda suka ci gajiyar shirin su dauka cewa Allah ne ya basu sa’a aka zabu su aka basu horon, ya bukace su da su tabbatar sun yi amfani da kayan aikin da kamfanin ya samar musu ta hanyar data dace.
Da yake jawabi, shugaban kula da ayyukan jin dadin jama’a na Dangote Cement Plc, Mista Wakeel Olayiwola, ya ce koyar da sana’o’in na daya daga cikin jerin ayyukan da kamfanin ke gudanar wa ga Mazauna Inda kamfanin yake, wanda ake aiwatarwa a fadin Afirka.
Mista Olayiwola ya bayyana fatansa na ganin cewa wadanda suka ci gajiyar shirin suma sun koyar da wasu ta yadda alkhairin zai yadu a tsakanin al’ummar Jihar Kogi.
Janar Manaja na ayyuka na musamman, Mista Ademola Adeyemi ya ce an zabo mata 10 10 daga Oyo, Iwaa, Apata, da Obajana, wadanda suka hada da masana’antar da masu hakar ma’adanai.
Mista Adeyemi ya ce shirin fasahar hadin gwiwa ne da hukumar kula da samar da ayyukan yi ta kasa (NDE).

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar NDE a Jihar Kogi, Abubakar Zakari, ya ce wadanda suka ci gajiyar shirin, sun samu horo mai inganci na tsawon watanni uku, a daidai lokacin da ya taya kamfanin murnar daukar nauyin koyawa mata sana’o’in da zasu dogara da kawunansu.
Sarakunan gargajiya daga masarautu daban-daban sun yabawa kamfanin bisa abin da suka bayyana a matsayin wani babban cigaba wanda zai bunkasa rayuwar al’ummar su.
Mai martaba, Olu-Apata, Oba Dr. Frederick D.O. Balogun, ya bayyana jin dadinsa tare da yin alkawarin ci gaba da baiwa al’ummarsa goyon baya ga kamfanin.
Da take jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Misis Titilayo Onimola, mai shekaru 33, ta yaba wa shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ta kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da ba shi goyon baya, ya kuma bunkasa harkokin kasuwancinsa.