INEC tace ta gamsu da yadda jama’a suka fito su ke karbar katin zabe

Date:

 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta bayyana gamsuwarta game da yadda mutane ke fitowa domin karɓar katin zaɓe da hukumar ke rabawa a fadin ƙasar.

 

Babban kwamishina a hukumar zaɓen kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a, Festu Okoye ne ya bayyana haka a wata zantawa da gidan talbijin na Channels TV.

 

Mista Okoye ya dangata fitowar jama’a da yadda shugabanni a matakai daban-daban ke wayar da kan jama’a game da fitowa karɓar katin zaɓen.

 

Talla

“Yawan ƙarbar katin ya bambanta daga wannan jiha zuwa waccan, kuma muna samun bayanai daga kwamishinoninmu da ke jihohin ƙasar daban-daban”, kamar yadda ya bayyana.

 

Haka kuma babban kwamishin a hukumar ya ce hukumar na fuskantar matsaloli game da mutanen da ba su san hanyar za su bi domin karɓar katin nasu ba.

 

Talla

Ya ce INEC ba za ta buga katin ga mutanen da suka yi rajista fiye da sau ɗaya ba, saboda a cewarsa har yanzu tsoffin katinsu yana aiki.

 

Amma ga waɗanda suka sauya wurin gudanar da zaɓe, za su iya samun katinan nasu a wuraren da ake karɓar katin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...