Daga Rukayya Abdullahi Maida
Al’ummar Tudun Wada Dankadai dake karamar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, sun shiga rudani biyo bayan karin jinin mai dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da wani likitan bogi ya yi ga mata mai fama da cutar zazzabin cizon sauro wato maleria.
Kadaura24 ta rawaito Jinin, wanda ake zargin yana dauke da cutar HIV an ce wani da ake zargin likitan bogi ne ya yi wa mara lafiyar Karin jini da shi .
Bayan haka, wani bincike da wani kwamiti na musamman ya gudanar kan ayyukan ma’aikatan lafiya na jabu a cikin al’umma ya nuna cewa akwai cibiyoyin kiwon lafiya da likitocin bogi suke gudanarwa har 130 a yankin .

A wata hira da manema labarai a Kano, Shugaban kwamitin dake kula da yankin Tudun Wada Dankadai, Alhaji Abubakar Musa Karafe ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa a cikin likitocin bogi 130, daya ne kawai ke da takardar shaidar kammala sakandare.
Jaridar The guidian ta rawaito cewa Alhaji Karafe ya jaddada cewa bayan binciken kwamatin ya kuma gano daya daga cikin ma’aikatan lafiyar wanda injiniyan lantarki ne wanda ya kuma mallaki asibiti mai gadaje takwas kuma yana kula da masu fama da cututtuka daban-daban a cikin al’umma.
Ya ce: “Abin da ya fi muni shi ne yadda daya daga cikin likitocin bogin ya yi wa wata mata da ta je asibitinsa domin neman maganin zazzabin cizon sauro, karin jini da jini mai dauke da Cutar HIV.

“Abin takaici ne yadda muka samu wani injiniyan lantarki yana aiki a wani asibiti mai zaman kansa, yana kula da marasa lafiya, yana ba da magunguna, yana karin ruwa da jini har ma da kula da mata masu juna biyu.
hukumar ta kaddamar da binciken ne biyo bayan korafe-korafen da mazauna yankin suka rika yi kan yawaitar asibitoci masu zaman kansu da kuma likitocin bogi wadanda rashin kwarewarsu ya jima yana jefa al’umma cikin mawuyacin hali .
Da aka tuntubi Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu (PHIMA), Usman Tijjani ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce gwamnati na daukar matakan da suka dace domin dakile faruwar hakan a nan gaba, da kuma magance tabarbarewar harkokin kiwon lafiya a yankin.
Tijjani wanda ya yi magana ta bakin Daraktan Ayyuka na ma’aikatar, Isa Isyaku, ya ce, ana ci gaba da gudanar da wani shiri na yaki da likitocin bogi domin magance faruwar irin wannan lamarin nan gaba.