Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Kwaminitin wayar da kan al’ummar karamar hukumar Kabo illar shiga bangar siyasa, a yayin babban zaban kasar nan na shekarar 2023 mai zuwa ya kai ziyara fadar mai martaba sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu domin gabatar da kan su dakuma bayyana masa aikin kwaminitin.
Da yake jawabi tun da farko a lokacin ziyarar shugaban kwaminitin wayar da kan al’ummar karamar hukumar Kabo illar shiga bangar siyasa a lokacin babban zaban kasar nan na shekarar 2023 mai zuwa Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, ya bayyana wa sarkin cewa shugabancin kungiyar yan kasuwa yan asalin karamar hukumar Kabo wato ( Kabo Zone Traders Association) dake a jahohi guda sha biyar dake fadin tarayyar kasar, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Salisu Adamu Kabo ne suka samar da kwaminitin domin bada gudummawar su.
Alhaji Mamuda Zangon Kabo yace, abun damu wa ne yadda ake samun wasu daga cikin matasan yankin karamar hukumar ta Kabo, Kano ta Arewa da kuma fadin jihar Kano na gaba da junan su a sakamakon banbancin ra’ayin siyasa ko kuma na jam’iyya.

Ya kara da cewa, tuni kwaminitin ya fara gabatar da shirye-shirye a kafafan yada labarai, ziyartar limaman masallatan juma’a, iyayen kasa domin taimaka wa yinkurin kwaminitin da yake a halin yanzu.
Daga bisani Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo yace, kwaminitin ya fara ganawa da wasu daga cikin yan takarar kujeru daban daban na bambanta jam’iyyu domin namufofin su ga al’ummar karamar hukumar ta Kabo da zarar sun samu dama a babban kasar nan mai zuwa, ya Kuma tabbatar da cewa kungiyar yan kasuwa yan asalin karamar hukumar ta Kabo dakuma kwaminitin wayar da kan al’umma illar shiga bangar siyasar baya goyan baya tallan wani dan takara kokuma goyan bayan wata jam’iyyar siyasa.

Shima da yake nasa jawabi sakataran kwaminitin wayar da kan al’ummar karamar hukumar ta Kabo illar shiga bangar siyasar a lokacin babban zaban kasar nan mai zuwa Alhaji Ibrahim Usman Kabo, ya shedawa sarkin cewa abun damuwa ne yadda wasu daga cikin yan siyasa ke amfani da matasa maza da mata wajan basu muggun kwayoyi a lokacin yakin neman zaba, kokuma tayar da hankulan al’umma a ranar zabe dakuma bayan zaban, abunda ya sanya kwaminitin ya tashi tsaye domin ganin yayi yaki da wannan dabi’ar.
Da yake karbar bankucin tawagar yan a fadar sa mai martaba sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya nuna farin cikin sa da ziyarar da kwaminitin ya kawo masa ya Kuma tabbatar da cewa masarautar Karaye a shirye take a ko wane lokaci domin ganin ta bada hadin kan daya kamata dan ganin kwaminitin ya cimma nasarorin daya sanya a gaba.