Lokaci ya yi da za a hukunta ‘yan siyasa masu ci-da-addini – El-Rufai

Date:

Daga Auwalu Alhassan Kademi

 

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.

 

Rahotonni sun ambato gwaman na wannan maganar ranar Talata a lokacin bikin ƙaddamar da babban ofishin ‘gidauniyar zaman lafiya da ci gaba’ ta mai alfarma sarkin musulmi

 

BBC Hausa ta rawaito El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini da su riƙa gudanar da addu’o’in samun ingantaccen zaɓe da samun zaman lafiya a fadin ƙasar.

 

Ya ce “Ina so na yi amfani da wannan damar na yi kira ga shugabanninmu da ke nan, masu girma sarakunan gargajiya da malamanmu da su ci gaba da yi wa ƙasarmu addu’o’in samun zaman lafiya da samun ingantaccen zaɓe, tare da yin addu’ar Allah ya zaɓa wa ƙasarmu shugabannin na-gari da za su haɗa kan ƙasar tare da ciyar da ita gaba”

 

”A matsayina na ɗan ƙasa, kuma gwamna sannan kuma musulmi bana jin daɗin yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci a matsayin makaminsu na yaƙin neman zaɓe”, in ji El-Rufai.

 

Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta waɗanda ke ƙoƙarin amfani da addinin a matsayin makamin yaƙin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...