Daga Khadija Aliyu
Wasu gungun mata ‘yan kasuwa, sun roki gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da su taimaka musu, dangane da shari’ar da ake yi a babbar kotun shari’a ta Kofar Kudu, kan rikicin sama da naira miliyan 500.
An dai fara shari’ar da ke tsakanin Halima Ibrahim (Leema) da Habiba Tijjani da wasu 30 a tun watan Satumban 2022 .
Kadaura24 ta rawaito gungun matan, sun yi ikirarin cewa sun baiwa wata mai suna Halima Ibrahim da aka fi sani da Leema, miliyoyin kudi, da nufin yin kasuwancin hadin gwiwa don sayo kayan kichin da kayan wasan yara a kasar China amma har yanzu ba su sami kayan ba.
Sun bayyana cewa, matar taki ba basu kayan kuma taki Mayar musu da kudaden su, hakan tasa suka kai ta kara kotun shari’a musulunci ta Kofar Kudu, wadda ke karkashin jagorancin Ustaz Khadi Ibrahim Sarki Yola.

Wasu daga cikin matan da suka zanta da gidan rediyon Najeriya, Fatima Abdullahi Shehu, Rashida Kardam, Aishatu Abubakar, Aisha Rabi’u da Habiba Tijjani, Hassana Bello daga Abuja, Adamawa, Katsina, Gombe, Kaduna sun bayyana cewa, yawancin wadanda abin ya shafa suna zaune ne a makwabta. Jihohi, kuma dole ne su je Kano, a duk lokacin da za’a yi zaman kotu.
Sun bayyana, akasarin matan an kama su, wasu kuma mazajensu sun sake su yayin da kimanin biyar daga cikin wadanda suka yi odar kaya suka rasa rayukansu sakamakon matsin da suka fuskanta daga kwastomominsu kan su maido da kudaden.
Kungiyar ta jaddada cewa Leema ta ci gaba da yin alkawarin raba kayan amma bayan wasu watanni ta bayyana cewa ba ta shirya yin hakan ba.
Sun jaddada cewa, Halima Ibrahim ba ta taba zuwa zaman kotun ba, wanda aka dage zaman a lokuta da dama, kasancewar sun kasance a gaban kotu a ranar Alhamis inda lauyoyin wacce ake kara Halima ba su halarci zaman ba.
Sun yi kira ga Khadi Ibrahim Sarki Yola da ya taimaka musu ta hanyar gaggauta yanke hukunci, inda suka ce a matsayinsa na alkali da ya tabbatar da gaskiya sun yi imanin cewa zai kai ga gano tushen lamarin.
“Muna kira ga gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje khadimul Islam da majalisar masarautar Kano da su kawo mana agaji saboda muna cikin mawuyacin hali, mutane da dama suna yi mana barazana, ba mu da kwanciyar hankali.”
Rediyo Najeriya ya tuntubi lauyoyin Halima Ibrahim, Barista Aliyu da Barista Yunusa, amma har zuwa lokacin hada wannan rahotonbbai amsa kiran waya da sakonnin tes da aka aika masa ba.