Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta fara zartar da hukunce-hukuncen Alkalin Babbar Kotun Shari’ar musulunci ta yanke wa Malamin na Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin aikata batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Kadaura24 ta rawaito cewa Alkalin Kotun, Malam Ibrahim Sarki Yola yayin da yake yanke hukuncin a ranar 15 ga Disamba, 2022 ya ce hukuncin da ya biyo baya ya zama dole don hana ci gaba da yi ko yada kalaman batanci ga Fiyayyen halitta S A W.
Justice Watch News ta tattaro cewa mataimakin Sheriff na babbar kotun jihar Kano ya zartar da hukuncin a jiya juma’a.

Yayin da wakilinmu ya ziyarci masallacin Ashabul Kahfi da ke Filin Mushe a karamar hukumar Gwale da Masallacin Jamiurrasul da ke Sabuwar Gandu a cikin birnin Kano a ranar Asabar din nan, ya lura da cewa masallatan biyu da makarantar na wanda aka yankewa hukuncin, an kulle su Kuma suna karkashin kulawar jami’an tsaro da ke dauke da manyan makamai.
Hakazalika jaridar Justice Watch ta tattaro cewa dukkan littafai 189 da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayar a lokacin shari’ar an kwace su tare da kai su zuwa dakin karatu na jihar Kano kamar yadda kotu ta bayar da umarni.
A kwanan baya a zantawarsa da manema labarai, babban mai shigar da kara na jihar Kano kuma kwamishinan shari’a Barista Musa Abdullahi Lawan ya gargadi jama’a kan bin umarnin kotu, yana mai jaddada cewa za a kama duk wanda aka samu ya saba wa umarnin kotun, kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Kotun ta kuma haramta yadawa ko karantar da wa’azin Malaman a duk kafafen sadarwa na zamani ciki har da gidajen rediyo da ke Kano.
Alkalin ya tabbatar da cewa an dauki matakin ne domin dakile yada kalaman batanci a cikin al’umma.
“Wanda aka yanke wa hukuncin yana amfani da masallatansa guda biyu da makarantarsa wajen bayyana yada akidarsa, inda yake bude littafansa ne don fadar abun da yake so.” Kotun ta bayyana