Daga Zakaria Adam Jigirya
Mai dakin dan takarar sanatan kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Hajiya Hauwa’u A A Zaura ta raba tallafin kayan abinci ga iyaye matan da mazajensu suka rasu suka bar musu marayu su dubu daya domin saukaka musu radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Hajiya Hauwa’u A A Zaura ta raba kayan Abincin ne a jiya juma’a a ofishin Hisbah dake karamar hukumar Nassarawa.
Hajiya Hauwa A A Zaura wadda Hajiya Binta Rabi’u Zaura wakilta ta bayyana tallafin wani bangare na jin kai da tausayawa irin na Mai dakin A A Zaura kuma ta tabbatar da cewa zata cigaba da irin wadannan ayyukan alkhairin idan Zaura ya sami damar zama Sanatan kano ta tsakiya.
Ta yi alkawarin idan Al’ummar Kano ta tsakiya suka zabi Mai gidan ta zasu mai da hankali wajen tallafawa marayu da masu karamin karfi domin su ne suka fi kowa bukata, don haka tasha alwashin kuautata rayuwar su data marayun da suke gabansu.
Daruruwan Marayu ne suka amfana da wannan tallafi, idan akai ta’akari da yawan iyayen marayun da suka amfana da tallafin.
Dagacin kawaji Mallam Abdulkaadir Dan Taura, da Shugaban J.T.I Alh Nura Gwagwarwa, da shugaban kasuwar sabon gari Alh. Bala na daga cikin mutanen da suka halarci taron rabon tallafin.