Saudiyya ta warewa Nijeriya gurbin alhazai 95,000 a Hajjin baɗi

Date:

Daga Maryam Ibrahim zawaciki

 

Hukumar gudanarwar masarautar Kasar Saudiyya ta bai wa Nijeriya gurbin mahajjata 95,000 a hajjin shekara mai zuwa na 2023.

 

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta fitar a shafinta na Intanet a yau Laraba.

 

Tuni dai hukumar ta fara karbar kudaden mahajjatan da ke shirin sauke farali a badi.

 

A hajjin bana dai an samu tsaiko, inda mahajjata da dama ba su samu damar zuwa Saudiyya ba sakamakon gaza samun jirgi da suka yi.

Talla

Sai dai daga baya NAHCON ta dora alhakin hakan a kanta, inda ta ce kamfanonin jiragen sama ne suka gaza cika alkawuran da suka dauka.

Hakan ne ya sanya hukumar jin dadin alhazan mayar wa da mutane da yawa kudaden da suka biya.

 

Ana dai sa ran Nijeriya za ta kammala shirye-shiryenta don gudun sake aukuwar abin da ya faru a hajjin bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...