Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar NNPP a zaben shekara ta 2023 Engr. Abba Kabir Yusuf ya ce ‘yan sanda ne basa daukar mataki shiya rikice-rikicen siyasa ke karuwa.
Abba K Yusuf wanda ake yiwa lakabi da Abba Gida-gida ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron zaman lafiya na Kano wanda rundunar ‘yan sandan jihar tare da hadin gwiwar AMG Foundation da sauran kungiyoyin farar hula a karkashin G31 suka shirya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu kuma ya aikowa kadaura24, Abba Gida Gida ya ce jam’iyyun adawa a Kano sun hada kai kan duk wani nau’i na barazana da batanci daga jam’iyyar APC mai mulki, yana mai bayanin cewa tana amfani da damar ta wajen cin zarafin wasu zababbun al’umma.

A cewar sanarwar, dan takarar gwamnan ya tuna yadda aka far mu su da ake zargin shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas da dansa Sani Abdullahi Abbas AKA (Ochi) ne suka shirya su.
“Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya ci gaba da ba da shawarar cewa, muddin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro ba su gudanar aiyukan su yadda doka ta tanada dan cika alkwarin da suka dauka na kama aiki.
A karshe sanarwar ta ce matukar hakan ta gagara to wajibi ne abar al’ummar jahar Kano su kare kansu kamar yadda doka ta bada dama.