Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara adadin kudaden da za a rika cirewa duk mako a asusun a kowane mako na daidaikun mutane da na kamfanunuwa zuwa Naira 500,000 da kuma Naira miliyan 5 .
Babban bankin na CBN ne ya bayyana haka a wata wasika da ya aikewa bankunan a yau Laraba.

Babban bankin ya ce ya yanke wannan shawarar ne bisa korafe-korafe da aka samu daga masu ruwa da tsaki.
Ƙarin bayani na nan tafe…