Daga Zakaria Adam Jigirya
Kungiyar Kano central social media dake yada manufofin jam’iyyar APC ta bayyana goyon bayan ta ga Dan takarar Sanatan kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Hon Abdulkarim Abdulsalam A A Zaura a matsayin Sanatan yankin a zaben shakara ta 2023.
Da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a wurin taro na L&Z dake birnin kano Shugaban kungiyar Sulaiman Ameer Rangaza yace sun zasu goyawa A A Zaura bayan ne saboda yadda ya jima yana taimakawa al’ummar jihar kano tun kafin jam’iyyar APC ta bashi takarar Sanata.
Yace akwai bukatar mutane irin su AA Zaura a zauren majalisar kasancewar sa kwararre ne ta fuskar mu’amalama Kuma yana da Ilimi da gojewar da zai iya kare hakkin al’ummar sa a cikin majalisar kasa.
” Mun zauna da dukkanin masu ruwa da tsaki da ya’yan wannan kungiya Kuma dukkanin mu kanmu ya hadu zamu yi aikin tallata manufofin Dan takarar mu na Sanata da jam’iyyar APC baki daya, don ganin sun lashe zaben shekara ta 2023 da ke tafe”. Inji Sulaiman Rangaza
“Mai girma dan takarar mu a madadin shugabannin wannan kungiya Muna baka tabbacin zamu yi aiki ba dare ba rana wajen yada manufofin ka a kafafen sada zumunta da muke amfani da su har sai mun ga kayi nasara a zaben shakara ta 2023 da ke tafe”.

Da yake nasa jawabin dan takarar Sanatan kano ta tsakiya a tutar jam’iyyar APC Hon. Abdulkarim Abdulsalam A A Zaura ya godewa shugabanni da ya’yan kungiyar bisa alkawarin da sukai na marasa masa baya a zaben dake tafe.
” Babu shakka wannan rana ce ta farin ciki a wajena Saboda yadda kuka nuna mana kauna tare da alkawarin goya mana baya, hakan ta tabbatar da irin nasarar da muke cigaba da samu a koda yaushe Babu shakka dole mu kara godewa Allah”. Inji A A Zaura
Dan takarar Sanatan ta Kuma bada tabbacin idan Allah yasa ya lashe zabe zai tabbatar ya cika dukkanin alkawauran da ya yiwa al’ummar kano ta tsaki, musamman batun tallafawa rayuwar mata da matasa da sana’o’i don su dogaro da kawunansu.
Taron ya samu halartar dan takarar sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC Hon. Abdussalam Abdulkareem Zaura (A.A Zaura) da daraktan yaƙin neman zaɓen sa Alh. Yahaya Garin Ali da shugaban jam’iyyar APC shiyyar kano ta tsakiya Hon Shehu Aliyu Ungogo da sauran manyan baƙi