Rikicin PDP : Kotu ta dage ranar yanke hukunci kan dan takarar gwamnan PDP a Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

 

A ranar litinin ne kotu ta sake dage shari’ar da aka dade ana jiran a yanke hukunci kan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP na jihar Kano a karo na biyu.

 

A zaman ta na yau, an sanar da masu masu kara da wadanda ake kara cewa za a yanke hukuncin ta hanyar na’urar gani-gaka wato Zoom, inda aka dage Zaman kotun zuwa ranar Alhamis mai zuwa 22 ga watan Disamba.

 

Justice Watch News ta rawaito cewa Alhaji Muhammad Abacha ne ya shigar da karar Inda yake rokon kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 25 ga Mayu, 2022.

 

Alhaji Muhammad Abacha ya kuma roki kotun da ta haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da jami’anta ci gaba da amincewa da Sadik Aminu Wali ko wani mutum a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano a zaben gwamna na 2023.

Talla

 

Ya shaida wa kotun cewa ya samu kuri’u masu rijaye a lokacin zaben fidda gwaniz, amma kuma INEC ta amince da Sadik Wali a matsayin mai rike da tutar jam’iyyar.

 

Hakazalika, a wata kara da Jafar Sani Bello ya shigar, inda yake kalubalantar Mohammed Abacha da Sadiq Wali kan zargin rashin cancantar su a matsayin yan takarar gwamna na PDP dogaro da kundin tsarin mulkin Najeriya, da dokar zabe da kuma kundin tsarin mulkin PDP.

 

Jafar Sani Bello, ya kalubalanci INEC kan amincewa da Sadik Wali a matsayin dan takarar PDP, sannan ya bukaci kotun ta shigar shi da shi cikin masu shigar da karar .

 

Rashin gamsuwa da hukuncin kotun, yasa Sadiq Wali ya garzaya kotun daukaka kara yana neman ta soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

 

A Saboda haka kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraren karar saboda bai kamata a hada shi da Wali a cikin karar ba.

 

Kadaura24 ta rawaito cewa lokacin da aka ci gaba da shari’ar a gaban babbar kotun tarayya a ranar 8 ga Disamba 2022, alkalin kotun ya sanya ranar 19 ga Disamba don yanke hukunci.

Hakazalika lokacin da aka ci gaba da shari’ar biyu a yau, an sanar da bangarorin cewa za a yanke hukuncin ta hanyar Zoom kuma daga baya an dage sauraron karar zuwa 22 ga Disamba, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related