Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Mukaddashin Darakta-Janar ta hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), Misis Christy Uba, ta yi kira ga ‘yan yiwa kasa hidima dasu kasance masu yada zaman lafiya don samar da hadin kan kasa a lokaci da kuma bayan kammala aikin su na yiwa kasa hidima.
Christy Uba ta yi kiran ne a yayin bikin rantsar da rukuni ‘C’ kashi na 2 na shekarar 2022 na yan yiwa kasa hidima, wanda ya gudana a sansanin NYSC dake Kusalla a karamar hukumar Karaye a jihar Kano.
Shugabar hukumar wadda ta samu wakilcin shugabar hukumar NYSC ta jihai kano, Hajiya A’isha Tata Muhammad, ta bukaci ‘yan NYSC din da su nuna matukar da’a da kuma inganta hadin kan kasa.
Ta kara musu kwarin gwuiwa da su yi amfani da damar da aka basu, wajen koyon sana’o’in dogaro da kai da za’a koya musu, a yayin zaman da zasu yi na tsawon makonni uku a sansanin.

Uwargida Uba ta bukaci masu yiwa kasa hidima da su guji amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labaran karya, da rura wutar kiyayya da sauran munanan aiyuka, maimakon haka su samar da wata hanya guda domin bunkasa hadin kan kasa da ci gaban kasa.
A nata jawabin, kodinetar shirin ta kano na jiha Hajiya Aisha Tata Mohammad wadda Daraktan sansanin Alhaji Bala Dabo ya wakilta ta ce an tsara shirin ne domin baiwa masu yiwa kasa hidimar gudanar da aikin hidimar kasa na shekara guda tare da koya musu darussa da sana’o’i kala-kala.
Ko’odinetan ta ci gaba da cewa an kimanin matasa 1,136 aka yiwa rajista a sansanin wanda 542 daga cikinsu maza ne da Kuma mata 594.