Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar Dattawan Arewa mai suna Arewa Consultative Forum (ACF), reshen jihar Kano ta gargadi ‘yan takarar gwamna da su guji tada zaune tsaye.
Shugaban kungiyar Dr Goni Faruk Umar ya yi wannan gargadin a jiya Lahadin yayin wata tattaunawa da ‘yan takarar gwamna a zaben 2023 da aka gudanar a Kano domin rage tashe-tashen hankula da tuni suka tashi.
A cewarsa, jigon zaman tattaunawa shi ne kungiyar taji abubuwan da ‘yan takarar suke so yiwa jihar kano idan aka zabe su.
“ Muka fada musu cewa za mu so su bamu tabbacin cewa idan sun ci zabe ba za su yi katsalandan a kason kudaden kananan hukumomi ba .

“Mun roke su da su da su tabbatar babu daya daga cikin ‘ya’yansu ko na kwamishinoninsu da zasu je kasashen waje neman ilimi, su tabbatar sun halarci makarantun gwamnati domin sanin matsalolin da fannin ilimi ke fama da shi don magance su.
“Ba ma tsammanin wani gwamna ko mataimakinsa ko kwamishinoni za su fita waje neman magani. Su tabbatar sun inganta fannin kiwon lafiya ta yadda kowa zai iya samun ingantaccen kiwon lafiya.
Mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Kwamared Aminu Abdussalam, ya ce ba su taba kin amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba, amma sun gabatar da wasu bukatu na cewa dole ne hukumomi su dauki matakin da ya dace kan duk wanda ya saba doka.
Ba za mu iya sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya ba a lokacin da a fili aka bar wasu mutane su yi rashin da’a kuma su ci gaba da haifar da tashin hankali a jihar Kano, za mu iya sadaukar da kanmu ne kawai idan muka ga an yi abin da ya dace tare da bin doka ba,” inji shi.
Yanayin siyasar Kano na kara zafafa ganin yadda jam’iyyar NNPP da APC mai mulki ke takun saka.
A mako mai zuwa ne ake sa ran ci gaba da zaman tare da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC kuma mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.