Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP a shekarar 2023, Abba K. Yusuf, na shirin kaddamar da manufofin sa da kuma kaddamar da kwamitin yakin neman zaben sa .
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, kuma ya aikowa kadaura24, ya bayyana cewa Abba Gida Gida zai kuma gabatar da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ga mutanen Kano a hukumance tare da kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa/Gwamna na jihar kano.

Bikin wanda ake sa ran zai gudana a ranar Talata 6 ga watan Disamba 2022 a Meena Event Centre, Kano, zai samu halartar shuwagabannin jam’iyyar, ‘yan kasuwa, malaman addini da kungiyoyin farar hula.