Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar kano tace za’a kammala aikin Samar da wutar lantarki mai zamanta ta jiha da ake gudanarwa a garin Tiga dake karamar hukumar babeji a ƙarshen wannan wata na Disamba da muke ciki.
Kadaura24 ta rawaito mataimakin Shugaban kwamintin da gwamnatin jihar kano ta kafa domin Samar da karin wutar lantarki a jihar kano Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi, ne ya bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar gani ga ido Madatsar ruwa ta tuga Inda a nan ne ake gudanar da aikin.
Rabi’u Sulaiman Bichi, yace aikin yana tafiya kamar yadda ya dace, Amma an Sami sauyin yawan adadin wutar da za’a samar daga Migawat 10 zuwa 6 da rabi.
yace an sami sauyin ne sakamakon yadda Madatsar ruwan ta jima a Babu yasa, Inda yace Masu gudanar da aikin wadanda suka zo daga kasar India sun bayyana cewa idan aka Samar da Migawat 10 na wutar lantarkin ruwan zai iya karewa cikin watanni 4.

” Wannan dalilin yasa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta Amince ayi aikin a haka, Saboda al’ummar jihar kano su dade suna amfanar aikin”. Inji Rabi’u Bichi
Yace Idan an kammala aiki za’a raba wutar ne ga futulin kan hanya daga cikin kwaryar birnin Kano, Inda ya bada tabbacin aikin zai taimaka sosai wajen kara inganta hasken wutar lantarki da ake da shi a Kano ,sannan gwamnatin jihar zata sami saukin kashe kudade wajen siyan man dizal.
” Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kashe magudan kudaden wajen gudanar da wanann aiki wanda zai magance Wani kaso na matsalolin hasken wutar lantarki da ake fuskanta a kano”. Inji shi
Rabi’u Sulaiman Bichi wanda yake tare da sauran yan kwamitin karkashin jagorancin Shugaban kwamintin wanda shi ne shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Usman Bala, ya ce gwamnati Kano ce kadai take gudanar da aikin ba tare da hadin gwiwar kowa ba.