Daga Abdulrashid B Imam
Gabanin zaben 2023 mai gabatowa, Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar NNPP mai wakiltar Kano ta Kudu, Rt. Hon. Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nada mataimaka biyu, wadanda za su gudanar da harkokinsa na yada labarai a lokacin yakin neman zaben sa.
Kawu ya nada Ashiru Shehu Kachako, gogaggen dan jarida mai gogewa na tsawon shekaru, a matsayin babban mataimaki na musamman na 1 akan harkokin yada labarai da Abbas Adam Abbas, matashi kuma hazikin dan jarida, a matsayin mataimaki na 2 na musamman kan harkokin yada labarai.

A wata sanarwa da shi da kansa ya sanya wa hannu a Kano ranar Asabar, Kuma ya aikowa kadaura24, Kawu ya ce ana sa ran sabbin mataimakan kafafen yada labarai guda biyu da aka nada za su yi amfani da kwarewar da suka samu tsawon shekaru a kan sabbin ayyukan da aka nada wajen karewa da yada manufofin sa a kafafen yada labarai.
“Ina mai matukar farin cikin sanar da Ashiru Shehu Kachako da Abbas Adam Abbas a matsayin SSA 1 da SA 2 akan harkokin kafafen yada labarai, na san dukkaninsu sun kware sosai a fannin yada labarai”. Inji Kawu
“Ina da kwarin gwiwar wadannan yan jaridu zasu iya jagorantar harkokin yada labarai na kwamitin yakin neman zaben takarar Sanatan kano ta kudu nan da watanni biyu masu zuwa yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa,” in ji Kawu a cikin sanarwar.
Ashiru Shehu Kachako kafin yi masa wannan nadin shi ne Shugaban sashin Kasuwanci na Gidan Talabijin na Sunnah TV Abuja. A baya ya kasance Babban Editan Jaridar Zuma Jaridar Hausa dake Kano da kuma Shugaban sashin Labarai da Shirya-shirye na DTV Online. Kachako ya kuma yi aiki a matsayin shugaban sashin addini, Edita kuma shugaban riko na tsare-tsare na gidan rediyon Vision FM Kano daga shekarar 2019 zuwa 2020, sannan ya rike irin wadannan mukamai a gidan rediyon Freedom dake Dutsen jihar Jigawa tsakanin 2007 zuwa 2019. Malami a Nasarawa. Makarantar Nursery and Primary School, Kachako daga 2005 zuwa 2006, Ashiru Kachako ya kasance sakataren cibiyar kiwon lafiya da injiniya ta Kachako daga 2004 zuwa 2007.
An haife shi a shekarar 1973, Ashiru Kachako ya yi Babbar Diploma (HND) a Office Technology and Management, Advanced Diploma a Mass Communication and Postgraduate Diploma in Education a Kano State Polytechnic. Ya kuma yi digirin digirgir (PGD) a fannin sadarwa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Yanzu haka yana karatun digirinsa na biyu a fannin sadarwa na jami’ar Bayero ta Kano.
Sabon mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai 2, Abbas Adam Abbas, dan jarida ne a gidan rediyon Nasara, Kano. Abbas ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato, inda ya yi BSc a fannin ilmin halittu.