Zan yiwa al’ummar Kura Madobi da Garun Mallam wakilcin da ba’a taba yi musu irinsa ba – Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

Daga Nura Abubakar

 

Dan takarar majalisar wakilai a yankin Kura Madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC Hon Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya Sha alwashin yiwa al’ummar yankin kyakyawan wakilcin da ba’a taba yi musu irinsa ba tun da aka dawo damakaradiyya.

 

” Zan Samar da wani tsari da zamu rika Jin bukatu da matsalolin al’umma donrmu domin kaiwa majalisa ko kuma mu nema daga gwamnatin tarayya ko ta jiha duk dai don ciyar da wannan yanki namu gaba”. A cewar Musa Iliyasu Kwankwaso

2023: Kungiyar Izala ta bayyana matsayarta kan wanda zai Shugabanci Nigeria

 

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24, don gane da yadda zai tunkari majalisar wakilai idan Allah ya sa al’ummar yankin sun zabe shi a 2023.

Talla

Musa Iliyasu Kwankwaso yace a bayan an zabi yan majalisar a wannan yanki namu Kuma sun yi iya abun da zasu iya, amma Ina da burin idan mutanen kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam suka zabe ni tabbas zasu Sabon salon wakilci ba irin wanda suka saba a baya ba.

 

” Kamar yadda naji ana fada bani da tabbas wai saboda muhimmancin noman da al’ummar mu suke yi, ana Saka duk dan majalisar su a kwamitin aiyukan Gona, to tabbas zan yi amfani da wannan damar don Kara habbaka aikin Gona tunda da shi al’ummar mu ta yi fice”. Inji Kwankwaso

 

Ya kara da cewa zai tabbatar da cewa yana sanar da al’ummarsa halin da ake ciki game da aiyukan mazabu da sauran aiyuka da zai kawo yankin ta hanyar amfani da kafafen yada labarai, domin al’umma Kura Madobi da garun Mallam Inda aka kwana da Inda aka tashi game da aiyukan da kudirorin da zai gabatar a majalisar.

 

Dama dai Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi fice wajen bayyana manufofida aiyukan duk gwamnatin da yake cikinta a kafafen yada labarai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...