Ko da tsiya-tsiya: Sha’aban Sharada ya bukaci jami’an tsaro su kama Abdullahi Abbas

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

 

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharada ya bukaci jami’an tsaro da su kama tare da gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na kano a gaban kotu bisa kalaman tunzura al’umma da yayi lokacin kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓe na dan takarar su.

 

Sha’aban Sharada wanda yanzu haka shi ne dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni a majalisar kasa, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin yakin kwamitin yakin neman zaben sa Abba Yusha’u Yusuf ya sanyawa hannu aka aikowa jaridar kadaura24 a birnin Kano.

 

Sanarwa ta ce kalaman na Abdullahi Abbas za su iya saka tsoro da firgici a zukatan al’umma da hakan zai sa su ƙauracewa fita jefa ƙuri’a.

Ƴan Sanda sun kama wani jigon jam’iyyar NNPP a Kano

Haka kuma sanarwar ta ce a lokacin da al’ummar jihar Kano su ka gaji da jami’yyar APC kuma su ke ƙoƙarin kawar da ita daga mulki, a lokacin ne kuma Abdullahi Abbas da aka sani da yin kalaman tayar da tarzoma ya ke amfani da kalaman da za su tayar da zaune tsaye.

 

Talla

 

Sha’aban Sharada ya ce kalaman na Abdullahi Abbas wani cin fuska ne ga al’ummar jihar Kano masu bin doka da oda musamman idan aka yi la’akari da yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta fitar da ƙa’idojin zaɓe da ake fatan gudanarsa cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ba a fahimci kalamaina na ko da tsiya-tsiya ba – Abdullahi Abbas

 

Hakazalika ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar ADP wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar wakilai, ya ce kalaman Abdullahi Abbas “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai mun ci zaɓe”, sun saɓa da sashe na 96 na kundin dokar zabe na shekarar 2022 da ya haramta yin amfani da barazana ko tursasawa ga masu kaɗa ƙuri’a..

 

A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi waɗannan kalamai a lokacin da suke ƙaddamar da kamfe ɗin takarar gwamna a Ƙaramar hukumar Gaya.

 

Ya kamata a Yan Sanda su kama Shugaban APC na Kano – Abba Gida-gida

A ƙarshe Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi kira ga jami’an tsaro da alhakin tabbatar da tsaro ya rataya a wuyansu da su gurfanar da Abdullahi Abbas ɗin a gaban shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...