Ba a fahimci kalamaina na ko da tsiya-tsiya ba – Abdullahi Abbas

Date:

 

Shugaban jam’iyyar APC reshan jihar Kano, Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen da ake masa na amfani da kalaman tunzura gangamin yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa.

 

Kadaura24 ta rawaito cewa Kalmar “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai mun ci zaɓe”, ba baƙon abu ne domin an sha jiyo Abdullahi Abbas na ambato wadannan kalamai a tarukan siyasa tun daga zaben 2019.

 

Ƴan adawa a jihar na cewa irin wadannan kalamai na Abdullahi Abbas, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da babban zaɓe da ke tafe a jihar.

 

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, shugaban APCn a Kano ya ce an yi wa maganganunsa mummunar fahimta ce kawai.

Talla

A makon da ya gabata ne BBC ta kawo rahoto kan zargin da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na yin kalaman tunzura rikici.

 

“Galatsi ne ga ‘yan hamayya”

 

“Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza ha-mata, ko me za a yi, ko me zai faru, ko mai tafanjama fanjam sai mun ci zaɓe.”

 

Shugaban jam’iyyar APC ya yi waɗannan kalamai ne a makon da ya gabata yayin da suke ƙaddamar da kamfe ɗin takarar gwamna a Ƙaramar Hukumar Gaya.

 

Sai dai a lokacin da BBC tayi masa tambaya kan dalilan amfani da wadannan kalamomi da ke kama da na tunziri rikici, sai ya ka da baki ya ce:

 

“Tsiya-tsiya takobi ce? Tsiya-tsiya mashi ne? Tsiya-tsiya wuƙa ce? Tsiya- tsiya bindiga ce? Ai dagewa ce lallai ka tsaya sai an ci zaɓe, abin da ake nufi kenan.

 

Abdullahi Abbas ya ce ai “abokan hamayyar mu shaƙiyanci ne, ai sun san abin da muke nufi, batu ne na jefa ƙuri’a kuma mu kuri’a da ake jefawa muke nufi da tsiya-tsiya, domin ita ce tsiyar ai da muke nufin zamu saka musu a zaɓe”.

Gobara ta kone wata makarantar firamare a kano

Shugaban na APC a Kano, ya ce wannan karon zaɓe ne za a yi falan ɗaya, domin a baya an sha su, sun kuma warke, “wai inconclusive bayan su sun san cewa cutarsu aka yi”.

 

Abbas ya ce yanzu waɗannan kalamai na shi na nufin ba za su sake bari a maimaita hakan ba a zaɓe mai zuwa. “Ba zamu bari a sake cutar mu ba”.

 

“Kalmomina ba sa tunzura rikici”

 

“Ni ba ni da ja da aƙidar dimokuradiya, domin kalmomina ba na husuma ba ne, ina da asali, na fito daga gidan sarauta, ina iya zama sarki, don haka ni ba mutum ba ne da zai so haddasa rikici”.

 

Abbas dai na nuna cewa kalmominsa hausa ce, kuma dama shi ɗan siyasa duk abin da ya ce sai na sauya ma sa.

 

A cewarsa siyasar Kano ta gaji haka, “mu ‘yan Kano haka muke siyasarmu, kalmominmu sun sha bamban kuma shi talaka da ake yi domin shi yasa me muke nufi.

 

Abbas ya tunasar da kan sa cewa ai ya taɓa yin waɗannan kalamai a baya, kuma babu wanda ya tunzura, kuma shi wai bai ce kowa ya ɗau makami ko ya yi fitina ba, kalamominsa na nufi a kasa a tsare kar ayi ma su maguɗi.

 

“A zaɓen baya mu aka yi wa maguɗi, mu fa mun fi son kowa ya zauna lafiya, kalmomina burga ce ta ‘yan siyasa”.

 

Da aka yi masa tambaya ko shin ba su da wani abin burga na jan hankali mutune su zaɓe su, sai ya ce, ba wai ba su da ayyukan raya kasa ba ne, kawai dai su hausawa sai da haka.

 

Ya kuma zargi cewa “ai su masu korafi ai nasu shaƙiyanci da iyayen gidansu ya fi nasu muni”.

 

Ya ce su ‘yan APC galatsine suke yi amma ga ɓarayin kuri’a wanda kowani talaka da abokin hamayya ya san abin da suke nufi.

 

Abbas ya ce sun haramta ɗaukan makamai da kalaman tunzuri, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci.

 

Siyasar ba ta da maraba kamar ta sauran duniya, kawai dai tunda batu ne na harshen hausa dole su yi ta yadda ‘yan jihar Kano hausawa za su fahimce su, in ji Abdullahi Abbas Kamar yadda BBC ta wallafa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...