Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar lahadi har ta kone wata makarantar tsangaya firamare ta kwana da ke kauyen Kiyawa da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa, gobarar ta lalata gaba daya ajujuwa 14 da ofisoshi 12 da bandakuna 21, dake cikin harabar makarantar.
Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta Bichi ta samu kiran gaggawa daga Alhaji Ghadafi Sani Bagwai.

Ya kara da cewa, da isar da tawagar jami’an hukumar wurin sun gano cewa wani gini mai tsawon kafa 400 zuwa 400 wanda ake amfani da shi a matsayin makarantar kwana ta Tsangaya Model, ya kone baki daya
Laifin Iyaye da shugabanni ne yasa matasa suke shiga bangar siyasa – Aminu Danjimmai
Saminu Yusif ya jaddada cewa, gobarar ta tashi ne daga babban ginin da ke kan hanyar sadarwa, bayan da na’urar hasken rana ta lalace, ta kuma bazu zuwa wasu sassan makarantar Tsangaya.
Jami’in hulda da jama’ar ya yi nuni da cewa, ba a samu asarar rai ba a lokacin da lamarin ya faru, domin an yi nasarar kwashe dukkan daliban tsangayar.
Ya jaddada jajircewar hukumar wajen kare rayuka da dukiyoyin mazauna Kano.