Mun yi nasara a shari’o’i fiye da 3,000 a 2022 – EFCC

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

 

Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa a Najeriya ta ce ta yi nasara a shari’o’i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin wata 11 na shekarar 2022.

 

Shugaban hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ƙwace kuɗi naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ƙasa waɗanda suka mayar wa gwamnati.

Talla

Kazalika, EFCC ta ƙwace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) – tsohon mataimaki na musamman ga tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki.

 

“Haka nan, mun yi nasarar ƙwace kadara 40 a Najeriya da Amurka da Landan da Dubai mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu,” in ji shi.

 

Mako biyu da suka wuce, wata kotu ta bayar da umarnin ƙarshe na ƙwace wasu kadarori biyu na tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison- Madueke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...